Kamfanin Facebook ya ce ba zai cire wanibidiyo da aka sauya muryar shugabansa Mark Zuckerberg ba daga Instagram, inda aka nuna shi yana bayyana wani kamfani a matsayin wanda ya yi sanadiyyar arzikinsa.
Sai dai bidiyon na bogi ne, kuma an hada shi ne da wata sabuwar fasaha da ke iya sauya murya da motsin baki.
A baya an soki Facebook saboda kin sauke irin wannan bidiyon inda aka sauya motsin bakin kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi.
Wanann matakin na baya-bayan nan ya zo dai-dai da sanarwar sababbin ayyuka 500 a Landan.
Kamfanin na sada zumunta ya ce akasarin sababbin ma'aikatan za su rika kirkirar manhajojin da za su rika ganowa da cire bayanai masu dauke da kalaman batanci ko janyo rarrabuwar kai a kan shafin.
Haka kuma, za su kirkiri hanyoyin da za su taimaka wa mutane wajen gane sakonni masu cutarwa.
An kirkiri bidiyon bogin Mista Zuckergerg ne don nuna wa a wani wajen bajen kolin kayan fasahar zamani mai suna Spectre a birnin Sheffield.
An shirya baje kolin ne don jawo hankali kan yadda ake sa wa mutane ido kuma ake iya sauya murya ko kamanni ko motsin baki a shafukan sada zumunta.
Ya kunshi hotunan fuskar shugaban kamfanin da aka kirkira a kan komfuta, sai aka hada da hoton bidiyon jikinsa da aka ciro daga wani hoton bidiyonsa da aka dauka a 2017 a shelkwatar Facebook da ke Silicon Valley.
Sai aka nadi muryar wani aka dora a kan bidiyon.
An dora bidiyon ne mai tsawon dakika 16 a Instagram ranar Asabar.
"Sakamakon abin da zai iya yiwuwa ne - idan aka kashe muryar," kamar yadda kafar ta fada.
"Muryar da aka sanya a bidiyon daga ji an san ba ta Zuckerber ba ce, sai dai ta wani ce mai kokarin kwaikwayo."
Zuwa yanzu an kalli bidiyon a shafin Instagram fiye da sau 25,000. An kuma yada shi a Facebook ma.
Masha Allah, Allah ya kara daukaka
ReplyDelete