AMIKO

TECHNOLOGY ON YOUR HAND

Saturday 1 June 2019

Yadda sabuwar jaruma ke hasashen zarce shaharar Ali Nuhu da Rahama Sadau



Wata sabuwar jarumar shirya fina-finan Hausa, Rahama Audu Ibrahim Kumo, da aka fi sani da Rahama Kumo a gajarce, ta bayyana cewa, tana ji a jikinta, za ta shahara fiye da jaruma Rahama Sadau da jarumi Ali Nuhu.

A tattaunawar Rahama Kumo da Legit.ng TV Hausa, a yayin da suke daukar wani sabon shirin mai suna 'Rayuwar Hanifa', a jihar Bauchi, ta ce, "Nima zan bi duk matakan da manyan jaruman suka bi, kamar Rahama Sadau, Ali Nuhu, Abdul M Sharif da sauransu har suka shahara, ina da yakinin wata rana zan fi su shahara."

Karanta cikakkiyar tattaunawa tsakanin Rahama Ibrahim Kumo da Legit TV Hausa:
Legit TV Hausa: Mai kallo zai so ya san takaitaccen tarihin ki, da kuma yadda aka yi har kika shigo wannan masa'anta ta Kannywood.
Rahama Kumo: Assalamu Alaikum jama'a, ni dai sunana Rahama A Ibrahim Kumo, an haife ni a garin Kumo da ke jihar Gombe, inda na yi karatun firamre har zuwa makarantar gaba da sakandire a cikin jihar.
Legit TV Hausa: Ga shi dai ke Likita ce, ko me ya ja ra'ayinki har kika yanke hukuncin shiga wannan masana'anta ta shirya fina finan Hausa?
Rahama Kumo: Gaskiya na so fina-finan Hausa tun ina 'Nursery School', tun ana kallo a gidanmu da TV mai baki da fari, kamar d

1 comment: